Kamfanin Meta ya sanar da shirin bayar da tallafin dala 700,000 domin tallafa wa sabbin kamfanoni da masu haɓaka fasaha a Najeriya da wasu ƙasashe shida, ciki har da Masar, Kenya, Afirka ta Kudu, Saudiyya, Turkiyya da Hadaddiyar Daular Larabawa.
Ana sa ran fara gudanar da shirin a shekarar 2027, inda za a tallafa wa masu ƙirƙirar hanyoyin magance matsaloli ta amfani da kayan aikin fasahar AI na Meta, ciki har da Llama, da kuma na'urorin fasaha masu sawa a jiki.
Meta ta sanar da shirin ne a taron AI da na'urorin fasaha na yankin Afirka, Gabas ta Tsakiya da Turkiyya (AMET), wanda aka gudanar a Istanbul.
Baya ga tallafin, Meta ta ƙaddamar da cibiyar AMET AI Impact Hub, wadda ke da burin koyar da mutane sama da miliyan biyar dabarun amfani da fasahar AI cikin shekaru uku masu zuwa. Shirin zai mayar da hankali kan koyar da AI, wayar da kan jama'a game da fasahar da kuma taimaka wa ƙananan da matsakaitan 'yan kasuwa su amfana da ita.
Ana sa ran Meta za ta fitar da cikakkun bayanai kan yadda ake neman tallafin da sharuddan cancanta kafin fara shirin a 2027. Masu sha'awar shiga za su iya bibiyar sanarwar kamfanin ta cibiyar AI Impact Hub.
来源:Tech Hausa · x.com